Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar,
"Labarai masu dadi da ke zuwa game da gwajin allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19), sun zama wani haske a karshen rami mai duhu da duniya ke ciki."
Ghebreyesus ya gudanar da taron manema labarai ta hanyar sadarwar bidiyo a helkwatar Hukumar da ke birnin Geneva na kasar Swizlan.
Ghebreyesus ya ce,sun gamsu tare d jin dadi kan yadda ake samun nasarar gwajin alluran riga-kafin cutar Corona da ake samarwa a kasashe daban-daban.
Ya gargadi cewar akwai bukatar a yi rabo na adalci ga kasashen duniya bayan kammala gwajin alluran riga-kafin.
Ghebreyesus ya kuma fadi cewar, a tarihi ba a taba samun wata annoba da aka samar da riga-kafinta cikin sauri kamar Corona ba.
Ya ce "Labarai masu dadi da ke zuwa game da gwajin allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19), sun zama wani haske a karshen rami mai duhu da duniya ke ciki. A ynzuu akwai fata nagari kan cewar alluran riga-kafin za su taimaka wajen kawo karshen cutar Corona a doron kasa."
Darakta Janar na WHO ya kuma kara da cewar an kai wani mataki mai inganci sosai a ayukan samar da riga-kafin da ake yi wanda abu ne da ya kamata kasashen duniya su tabbatar.