Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewar daga cikin alluran riga-kafin Corona guda 180 da ake samarwa a duniya a yanzu, an yi gwajin 35 daga ciki a kan mutane.
Darakta Janar na WHO Dr. Tedros Adhanov Ghebreyesus a yayin gudanar da taron manema labarai ta hanyar sadarwar bidiyo a Cibiyar Hukumar da ke Geneva Babban Birnin Swizalan ya ce, tun a watan Maris aka fara aiyuka tukuru don ganin an samar da ingantaccen maganin riga-kafin Corona.
Ghebreyesus ya ce ya zuwa yanzu ana kan samar da magungunan riga-kafin cutar Corona (Covid-19) har guda 180, kuma an yi gwajin 30 daga ciki a kan mutane.
Babbar Likita da ke aiki tare da WHO Dr. Soumya Swaminathan ta ce a watan Yuli aka fara gwajin wasu alluran riga-kafin na Corona, kuma nan da karshen shekara za a iya samun sakamakon ko da na wucin gadi ne.
Swaminathan ta ce kafin a kai wani magani kasuwa sai an jarraba shi na akalla watanni 6 don tabbatar da ingancinsa.