WHO: A yaki da Korona da sauran rina a kaba

WHO: A yaki da Korona da sauran rina a kaba

Jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya sun bayyana cewa cutar ta coronavirus da sauran rina a kaba kuma "ayyukanmu" ne zai tabbatar da karshenta.

A cikin bayanan hadin gwiwa da Hans Kluge, darektan yankin WHO a Turai, da Batyr Berdyklychev, wakilin kungiyar a Turkiyya, suka jaddada cewa bai kamata mu yi sakance kyale samun bulluwar cutar da haifar da mace-mace ba.

"Mun kasance cikin wannan matsayi a lokacin bazarar da ta gabata. Lokacin da aka sassauta dokokin da aka sanya cikin sauri a wasu ƙasashen Turai, mun ga karin yaduwar cutar  da mace-mace a duk faɗin yankin Turai.

Sanarwar ta yi  gargadin cewa "duk da cewa ana. ci gaba da yin allurar rigakafin a duk fadin yankin Turai, akwai mutane da yawa da ba'a yiwa allurar ba kuma ana ci gaba da samun yaduwar cutar.


News Source:   ()