Sakamakon sace-sace da tashe-tashen hankula a Jamhuriyar Afirka ta Kudu, ana fuskantar karancin mai a wasu sassan lardunan Gauteng da Kwazulu Natal.
Tarzomar, wacce aka fara a ranar 9 ga watan Yulin, da neman a yiwa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma da ke daure afuwa, ta kai mako guda ana gudanar da ita.
Mutane da yawa sun rasa rayukansu kuma an tsare daruruwan mutane a yayinda tarzomar.
An wawushe manyan kantuna, shaguna da wuraren kasuwanci a tsakiyar lardunan Gauteng da Kwazulu Natal.
A wasu yankuna an samu karancin mai sakamakon farmakan masu dibar ganima suka kai musu.
An bayyana cewa a Durban, wanda shi ne mashigar Afirka ta Kudu zuwa Tekun Indiya, matsalar karancin abinci ya bayyana saboda satar dukiya da aka rinka yi a kantunan yankin.
A cewar kafar yada labaran News 24, an samu dogon layi domin sayen abinci a gaban shagunan da wawasar ba ta shafa ba.