A Amurka, ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdin.
Daruruwan mutane sun taru a gaban ofishin jakadancin Isra'ila dake Washington tare da nuna goyon baya ga Falasdin, sun kuma mayar da martani ga Amurka dake baiwa Isra'ila goyon baya a hare-haren da take kaiwa Falasdin.
Masu zanga-zangar dauke da tutar Falasdin sun dinga daga allunan da aka rubuta "'Yanci ga Falasdinwa", "'Yanci ga Gaza", "Isra'ila Kasar Ta'addanci" da kuma "Muna son Adalci yanzu-yanzu".
A yayin zanga-zangar an kira sunayen dukkan yara kanana Falasdinawa da Isra'ila ta kashe, an kawo makaru da aka nannade da tutar Falasdin inda aka bayyana yadda a kowacce rana Falasdinawa fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba suke mutuwa sakamakon hare-haren ta'addanci na Isra'ila.
A jawabin da aka yi an mayar da martani ga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Kasar Amurka Joe Biden, an kuma bukaci Amurka da ta kawo karshen taimakon da take baiwa Isra'ila a bangaren soji.
Wasu jama'ar sun taru a gaban karamin ofishin jakadancin Isra'ila dake New York inda suka mayar da martani game da hare-haren da ake kaiwa Zirin Gaza da aka yiwa kawanya.
A Atlanta, Houston da Los Angeles ma jama'a sun taru a gaban kananan ofisoshin jakadancin Isra'ila tare da gudanar da zanga-zanga. Haka zalika a Dearborn, Dallas, Baltimore da sauransu ma an gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdin.
Daga cikin kungiyoyin da suka shiga zanga-zangar tare da da neman Amurka ta daina taimakawa Isra'ila, har da wata kungiyar Yahudawa dake Amurka mai suna "If Not Now".