Wata Bafalasdiniya ta sake haduwa da danginta bayan shekaru 24

Wata Bafalasdiniya ta sake haduwa da danginta bayan shekaru 24

Wata Bafalasdiniya da ba za ta iya fita kasashen waje ba saboda kin ba ta katınta na shaidar zama 'yar kasa da Isra'ila ta yi, ta yi nasarar sake haduwa da danginta a Jordan bayan shekaru 24.

Sena Mohammed ta hadu da iyalinta a gefen gabar Kogin Jordan, wanda ke tsakanin Jordan da Yammacin Kogin da aka mamaye. Ta daga hannu daga nesa ba tare da ta sami damar ta rungume su ba.

Mahukuntan Isra’ila ba su bar Mohammed, wacce ta fara zama a gabar yamma da Kogin Jordan bayan aurenta ta ziyarci iyalinta a Jordan bisa dalilan cewa ba ta da katin shaidan zama 'yan kasa.

Mohammed na daya daga cikin Falasdinawa dubu 50 da Isra’ila ba ta ba da izinin katin shaidan zaman 'yan kasa ba. Lamarin dake hana dangi ganawa da 'yan uwansu.

 


News Source:   ()