Wata ɓaraka ta kunno kai a tsakanin Isra'Ila da Majalisar Dinkin Duniya

Wata ɓaraka ta kunno kai a tsakanin Isra'Ila da Majalisar Dinkin Duniya

Takaddama ta barke tsakanin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Isra'ila bayan da ƙasar ta umarci hukumar da ta kwashe kayayyakin na aikin lafiya a asibitoci dake yankin Gaza, bayanin da Isra'ila ta musanta.

Shugaban hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, hukumar ta WHO ta samu sanarwar daga sojojin Isra'ila cewa ya kamata su kwashe kayansu daga ma'ajiyar magunguna da ke kudancin Gaza cikin sa'o'i 24.

Adhanom ya  bukaci Isra’Ilar data dakaatar da ruwan wuta da take yi a kan asibitoci domin baiwa waɗanda suka jikkata damar samun kulawa da ta dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)