Kawo yanzu dai an ciro gawarwaki akalla 19 daga kogin, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.
Bayanai sun ce akwai 'yan wasan tseren Amurka na kasashen Amurka da Rasha da ke cikin mutanen da hatsarin jirgin ya rutsa da su.
Masu aikin ceto na ci gaba da laluben mutanen da suka nutse a ruwa.
A halin yanzu dai, hukumomin da abun ya shafa, sun dakatar da kamfanin jiragen sama na Ronald Reagan Washington na wani dan lokaci, yayin da ake binciken abin da ya haifar da hatsarin jirgin.
Rahotanni sun ruwaito cewa, jirgin saman ya tarwatse bayan faduwarsa tare da nutsewa a cikin ruwa, yayin da aka hango jirgin saman sojin mai saukar ungulu na yawo a saman ruwan.
Jirgin samfurin CRJ700, ya taso ne daga Wichita, inda ya nufi Kansas dauke da fasinjoji 60 sai kuma ma'aikatansa hudu.
Hukumomin Amurka sun ce, jirgin mai saukar ungulu samfurin H-60, ya tashi ne daga Belvoir da ke Virginia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI