Wasu jerin hare-haren makamai ta sama sun kashe mutum 52 a Gaza

Wasu jerin hare-haren makamai ta sama sun kashe mutum 52 a Gaza

Wasu majiyoyin lafiya sun faɗawa kafar Aljazeera cewa harin ta sama ya kashe mutum 12 ciki har da yara a tudun mun tsira dake al-Mawasi dake kudancin Khan Younis.

Ministan cikin gida na Gaza ya yi Allah wadai da kisan inda ya ce jami’an ƴan sanda biyun da suka mutu suna kan aikin bada agaji ga jama’a.

Ministan ya zargi Isra’ila da ta’azzara lamurra da jefa rudani da wahala ga alummar a Gaza sakamakon hare-haren ta sama da ta kai.

Wani bidiyo ya nuna mutane 15 ɗauke da raunuka yayin da wasu ke laluben waɗanda ke da sauran numfashi a cikin tantunan da suka yi kaca-kaca tare da ƙone ƙurmus.  

Isra’ila ba ta yi gargaɗi ba kan harin na yau Alhamis da ta kai al-Mawasi  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)