Falasdinawa hudu da ke gidajen kurkukun Isra'ila sun fara yajin cin abinci don nuna rashin amincewa da cigaba da "tsarewar da ake yi musu."
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da kungiyar fursunonin Falasdinu ta fitar, an ba da bayanai game da fursunonin Falasdinawa 4 da ba su amince da "tsarewar da aka yi musu ba" sabili da haka suka fara yajin cin abinci a makon da ya gabata.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa Isra’ila ta bayar da umarnin tsare dan gwagwarmayar Falasdinawa Mohammed al-Zagir, mai shekar 34, mahaifin yara uku wanda aka tsare shi a kurkukun Isra’ila tun watan Afrilun 2020 kuma ya kasance cikin yajin cin abinci tsawon kwanaki uku.
An bayar da rahoton cewa, Salim Zeydat, daga garin al-Halil a Zirrin Gaza, an kame shi a watan Fabrairun 2020, kuma duk da kammala wa'adin watanni hudu da aka yanke masa har yanzu yana tsare a kurkukun Isra'ila, lamarin da ya sanya shi fara yajin cin abinci.
An bayyana cewa, Muhammed Munir Imar, daga garin Tulkarim a arewacin Yammacin Zirrin Gaza, yana tsare tun a watan Oktoban shekarar 2020 kuma ya fara yajin cin abinci.
An lura cewa, Mujahid Mahmud Hamid, daga garin Ramallah da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan, yana tsare tun watan Satumbar 2020 kuma ya fara yajin cin abinci.