Wasu daga cikin muhimman matakan da shugaba Trump ya dauka a cikin wata guda

Wasu daga cikin muhimman matakan da shugaba Trump ya dauka a cikin wata guda

Korar baƙin haure, tsaurara matakan haraji, batun yaƙin Rasha da Ukraine, da kuma rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza, sune manyan batutuwan da suka fi daukar hankali a cikin matakan da shugaban ya dauka.

An gano dai yadda aka rika dibar bakin da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba ana tasa ƙeyarsu zuwa kasashen su na asali, inda a halin yanzu, ‘yan cirani sama da 8,768 aka cafke, tare da tasa ƙeyar 5,693 zuwa kasashen Mexico da Venezuela, da Indiya, da Columbia, Guatemala da kuma Ecuador.

Batun tsaurara haraji shine ya fi daukar hankali, musamman yadda ya sanyawa kasashe irin su China da Mexico da kuma Canada kaso mai yawa.

Baya ga wannan, furucin da shugaban na Amurka ya yi na cewa ya kamata a kwashe al’ummar yankin Gaza tare da sauya musu matsuguni zuwa kasashen Jordan da Masar, da sunan zai sake gina yankin, abin da ya haifar da tofin alatsine daga kasashe musamman na yankin Gabas ta Tsakiya.

Haka zalika, gwamnatin Trump ta shirya zaman tattaunawa ta musamman a Saudiyya game da rikicin Rasha da Ukraine, karon farko kenan da shirya irin wannan zama tun bayan kusan shekaru uku da fara yaƙin.

Ba a iya nan shugaban ya tsaya, domin kuwa ya cire ƙasar daga yarjejeniyar yanayi ta Paris, da cire ta cikin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya dakatar da USAID daga bayar da aikin tallafin da ƙasarsa ke yi, abin da ake ganin zai haifar da illa mai munin gaske ga kasashe masu tasowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)