Mutum 1 ya rasa ransa, wasu 10 sun jikkata sakamakon fashewar wasu abubuwa a titin Al-Zawiya na Zirin Gaza.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Gaza ta fitar ta bayyana cewa, an ji karar fashewar wasu abubuwa daga wani gidan bene da ke titin Zawiya.
Sanarwar ta ce an kai wanda ya mutu da wadanda suka jikkata a fashewar zuwa asibiti, kuma an samu asara a gidan da fashewar ta afku da mokotansa.
An bayyana kammala kashe gobarar da ta kama bayan fashewar abubuwan a gidan, an kuma fara gudanar da bincike.