Mutane 11 sun samu raunuka sakamakon wasu abubuwa da suka fashe a wata masana'anta da ke kudu maso-gabashin Bangkok babban birnin Taylan.
Fashewar ta afku a wani kamfanin sarrafa robobi da ke Bang Phli a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Suvarnabhumi.
An bayyana jikkatar mutane 11 sakamakon ibtila'in. Mutum 1 na cikin mawuyacin hali.
Mahukuntan filin tashi da saukar jiragen sama na Suvarnabhumi da aka jiyo karar fashewar sun bayyana cewa, ba a samu tsaiko ba wajen tashi da saukar jirage.
Ba a fitar da wata sanarwa ba dangane da ko meye ya janyo fashewar.
Ana ci gaba da aiyukan ceto da kubutar da leburorin da ke aiki a masana'antar.