Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar da ta afku a wani gida a Yukren.
Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewar an samu fashewar a wani gida da ke a gini mai hawa 9 a unguwar Poznyaki ta Kiev Babban Birnin Yukren.
Fashewar ta lalata gidajen da ke tsakanin hawa na 4 da na 7 na ginin.
'Yan sanda da jami'an lafiya da suka kai dauki wajen sun kubutar da mutane 21.
Shugaban gundumar Kiev Vitaly Klichko da ya je wajen ya bayyana an fara gudanar da binciken gano musabbabin fashewar.
Amma jami'an 'yan sanda na zargin dayan biyu, ko dai fashewar iskar gas ko kuma ta abubuwan fashewa masu kama da bam.