Wasu abubuwa sun fashe a sansanin sojin Hashdi Sha'abi da na gwamnatin Iraki da ke Bagdad Babban Birnin Kasar.
Rubutacciyar sanarwar da kafar yada labarai ta gwamnatin Iraki ta fitar ta ce "Wasu abubuwa 2 sun fashe a sansanin sojin Iraki na Sakar da ke kan hanyar Bagdat-Hille."
Sanarwar ba ta bayar da musabbabin fashewar abubuwan ba.
An dauki tsauraran matakan tsaro a sansanin da kewayensa da ke kudu maso-yammacin Bagdad.