Mutane 2 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wasu abubuwa a garin Lahor na Pakistan.
Jaridun kasar sun bayyana cewa, wasu abubuwa da ba a san meye ba sun fashe a yankin Johar Town na garin Lahor.
Mutane 2 sun mutu, wasu 17 sun jikkata sakamakon fashewar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, abubuwan da aka makala a jikin wani babur da ba a san wa ya ajje shi ba ne suka fashe.
An aika da jami'an tsaro da motocin daukar marasa lafiya zuwa yankin.