Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Turai(ESA) ta bayyana cewa, wani bangare na dusar kankara dake tekun Weddel ya ballo a yankin Antartika, inda ya zama dunkulen kankara mafi girma a duniya.
Dunkulen kankarar mai suna A-76 na da fadi da zagaye mai girman kilomita dubu 4,320 kuma yana da tsayin kilomita 175.
A-76 ya ballo daga tuddan kankara na Ronne, kuma a karon farko Binciken Ingila a Antartika ne ya fara gano shi.
Haka zalika tauraron dan adam na Copernicus Sentinel-1 ya hango tudun kankarar.