A arangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaro da wasu gungun masu dauke da makamai a lardin Sistan-Baluchestan da ke kudu maso gabashin Iran, sojoji 4 daga sojojin juyin juya halin Musulunci sun rasa rayukansu.
A cewar labarin kamfanin dillacin labarai na Iran ta IRNA bisa ga rubutacciyar sanarwar hedkwatar Kudus na Sojojin kare juyin juya halin Musulunci, rikici ya barke tsakanin jami'an tsaro da wasu gungun masu dauke da makamai a garin Hash na lardin Sistan-Baluchistan.
Sakamakon rikicin, sojoji 4 daga sojojin kare juyin juya halin Musulunci sun mutu.
Babu wani cikakken bayani da aka bayar game da kungiyar masu dauke da makamai da suka yi arangama da jami'an tsaro.