Wani mutum ya yi fama da Korona na tsawon shekara guda a Birtaniya

Wani mutum ya yi fama da Korona na tsawon shekara guda a Birtaniya

An samu wani dan kasar Birtaniya mai shekaru 72 da ya yi fama da kwayar cutar Korona na tsawon shekara daya.

Mai koyar da tukin mota da ya yi ritaya Dave Smith, wanda aka yi amannar ya kasance wanda ya yi fi kowa dadewa yana fama da kwayar cutar Korona a duniya, ya kasance dauke da kwayar cutar na kwana 305.

Ya shadawa kafar yada labaran BBC da cewa na kasance ina tari na tsawon awanni biyar inda ya na yanke kaunar ba zan rayu ba.

"Na kasance a shirye na ba da kai, na ce wa Lyn matata 'bari na tafi,"

Smith yana da wani yanayin rashin lafiya wanda ya haifar masa da raunin tsarin garkuwar jiki,  ya bayyana cewa ya kasance cikin yanayin da yake ganin mutuwarsa ta fi rayuwarsa.


News Source:   ()