An sanar da cewa wani mai neman tada zaune tsaye da ba'a san ko wanene ba ya yarda gawar alade a cikin farfajiyar wani masallaci dake garin Bratunac a gabashin Bosniya da Herzegovina.
Wacannan bakar aniyar tada zaune tsaye da ta faru a yankin jamhoriyar Serb wanda daya ne daga cikin yankuna biyu a kasar inda mafi yawan Sabiyawa ke zama ya janyo yin tir da lamarin daga Musulmin Bosniya.
Limamin Masallacin Elvir Hodzic ya bayyana cewar sun farga da gawar dabbance a lokacin sallar Azuhur wanda daga farko suka dauka ko na kare ne amma kusantarsa suka tabbatar da cewa gawar dan alade ne kudaje ke bi.
Ganin hakan ya sanya suka sanar da hukumar 'yan sanda nan take. Ya kara da cewa ma'aikatar fadar magajin gari sun zo sun dauki gawar aladen daga farfajiyar Masallacin inda ake alwala.
Garin Bratunac ya kasance garin dake yankin da aka yi kisan kiyashi a yakin shekarar 1992-1995 wanda keda yawan Musulmi fiye da dubu 21 amma a halin yanzu basu wace dubu 7 ba.