Wani jirgin dakon kaya mallakin Rasha ya nutse a tekun Mediterranean

Wani jirgin dakon kaya mallakin Rasha ya nutse a tekun Mediterranean

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce jirgin ya nutse ne bayan wata fashewa a cikin injinsa, sai dai an yi nasarar ceto mutane 14 daga cikin ma’aikatansa 16 da ke cikin jirgin yayin faruwar haɗarin.

A cewar sanarwar tuni aka isar da mutanen da aka ceto daga tekun zuwa Spain don basu kulawar gaggawa a gefe guda ake ci gaba da laluben 2 daga ciki da suka ɓace.

Wasu na’urorin naɗar bayanan hada-hadar jirgin na Rasha ya nuna yadda ya taso daga tashar jiragen ruwa ta birnin Saint Petersburg a ranar 11 ga watan Disamban nan yayinda ya aike da alama ta ƙarshe a jiya Litinin da misalin ƙarfe 22:04 agogon GMT.

Jirgin wanda mallakin kamfanin SK-Yug ne da ke matsayin wani ɓangare na Oboronlogistics bayan da ya bar Saint Petersburg ya nuna alamun yada zango a Vladivostock saɓanin tashar jiragen ruwa ta Tartous da ke Syria da bisa al’ada ya saba yada zango, amma kuma bayan kama hanya sai ya sauya matsaya.

Har yanzu dai babu amsa daga dukkanin kamfanonin biyu game da nutsewar jirgin wanda bayanai ke cewa yana ɗauke ne da wasu kayakin amfanin tashar jiragen ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)