Wani harin Rasha a Ukraine kan wani asibiti ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7

Wani harin Rasha a Ukraine kan wani asibiti ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7

Rahotanni daga yankin na bayyana cewa harin na farko ya kashe mutum 1 tare da lalata wasu benaye na wani asibiti, wanda ya kai hukumomin yankin soma kwashe marasa lafiya da ma'aikata, in ji ministan harkoki cikin gida na Ukraine Igor Klymenko a kan Telegram.

Yan lokuta da soma kwashe wadanan mutane ,Rasha ta sake kai wani sabon hari, a cewar Igor Klymenko. Ga baki daya mutane 7 ne suka mutu wasu 12 suka samu rauni.

Wani yankin Ukraine da Rasha ta kai hari Wani yankin Ukraine da Rasha ta kai hari REUTERS - Stringer

Rundunar ‘yan sandan kasar ta Ukraine ta ce tagwayen hare-haren sun yi muni, yayin da masu gabatar da kara suka ce an kashe dan sanda guda daya kuma ya jikkata. Rundunar ‘yan sandan kasar ta rubuta a kafar sadarwa ta Telegram cewa duka hare-haren biyu an kai su da jiragen sama.

Masu gabatar da kara na yankin sun ce harin na farko ya faru ne da misalin karfe 7.35 na safe agogon GMT, inda aka nufi asibitin da ake da marasa lafiya 86 a lokacin da kuma ma’aikata 38. Inda suka sake bayyana cewa harin na biyu ya faru ne da misalin karfe 8.25 na safe (0525 GMT) a wani lokaci da masu aikin ceto da 'yan sanda ke cikin aiki na kwashe marasa lafiya a wurin.

Dakarun Ukraine na mayar da martani Dakarun Ukraine na mayar da martani © AP

Kamfanin dillancin labaran Suspilne na kasar Ukraine ya buga hotuna daga wurin da lamarin ya faru da ke nuna gawarwaki da dama a kwance a kan titin kuma rufin ya balle daga ginin asibitin. Kungiyar sa kai ta Dobrobat da ke taimakawa gyara gidajen da suka lalace, ya rubuta a shafin sada zumunta cewa ‘yan sa kai na aikin a wurin lokacin da aka kai harin na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)