Mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon rushewar wani gidan otel a garin Suzhou na jihar Jiangsu da ke China.
Ana ci gaba da aiyukan kubutar da mutane daga karkashin buraguzan ginin.
Sanarwar da aka fitar daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu an ciro jikkunan mutane 8 da suka mutu kuma ana ci gaba da aikin ceton.
Sanarwar ta kara da cewa, an kubutar da wasu mutanen 14 inda ake ci gaba da neman wasu 9 da suka bata.
A shekarar 2014 aka bude gidan otel din mai dakuna 54.