Wani dan bindiga ya kashe 'yan kasar Lebanon biyu a Iran

Wani dan bindiga ya kashe 'yan kasar Lebanon biyu a Iran

An sanar da cewa wani dan bindiga dadi saman babur da ba'a san ko wanene ba ya kashe wasu 'yan kasar Lebanon biyu sanadiyar bude musu wuta da ya yi a Tahran babban Iran.

Kafar talabijin din kasar Iran ta yada labarin da ta karbo daga ma'aikatar tsaron kasar, inda take cewa wani dan kasar Lebanon dan shekara 58 mai suna Ahmed Dawud da 'yarsa yar shekara 27 mai suna Meryem Davud sun rasa rayukansu sanadiyar bude musu wuta da wani saman babur ya yi a yayinda suke cikin mota suna tafiya akan titin Pasdaran dake Tahran babban birnin Iran.

An bayyana cewa ana ci gaba da bincike game da lamarin.


News Source:   ()