Wani abin fashewa tun na lokacin yakin Iran-Irak ya tashi

Wani abin fashewa tun na lokacin yakin Iran-Irak ya tashi

An sanar da cewa fashewar wani abu ya yio sanadiyar rayukan mutum uku a yammacin kasar Iran.

A jihar Ilan inda ake ganin an bar wani abin fashewar da aka yi aiki dashi tun lokacin yakin Irak-Iran ne ya fashe tare da hallaka mutum uku da kuma raunana mutum uku.

Yaki tsakanin Iran da Irak ya fara ne a ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 1980 wanda tare da hukuncin Mjalisar Dinkin Duniya mai sakin layi 598 sunka kawo karshen yakin a ranar 20 ga watan Agustan shekarar 1988.

Abubuwan fashewar da suka fadi a kasahen biyu a lokacin yakin har ila yau ana samun tashinsu a dukkanin kasahen biyu tare da kashe da kuma raunana al'umman kasashen.

 


News Source:   www.trt.net.tr