Wadanda suka rasa rayukunsa sakamakon girgizar kasar Indonesiya sun haura 46

Wadanda suka rasa rayukunsa sakamakon girgizar kasar Indonesiya sun haura 46

Yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasar da ta afku a yankin garin Majene dake jihar Yammacin Sulawesi a kasar Indonisiya sun haura mutum 46.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ce ta sanar ta bakin shugabanta Raditya Jati da cewa a yankin mamuju mutum 37, Majene 9 kawo yanzu wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar gurgizar kasar sun haura 46.

Jati ya kara da cewa yawan wadanda suka raunana kuma sun kai 826.

Raditya Jati ya bayyana cewa, bisa ga sabon bayanin da suka samu, gine-gine 415, gami da cibiyoyin gwamnati kamar asibitoci,da tashar jiragen ruwa, sun lalace, kuma ana ci gaba da bincike da ceto a cikin gine-ginen da suka lalace.

Hukumar Kula da Yanayi,  (BMKG) ta sanar a jiya cewa girgizar kasa mai karfin 6.2, wacce ta afku a zurfin kilomita 10 da fadin kilomita 6 a arewa maso gabashin garin Majene, an kuma ji alamunta a biranen Palu da Makasar da karfe 01.28.

 


News Source:   ()