Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya sanar da cewa a kasarsa an kama wani dan leken asiri dan kasar Amurka a yankin matatar mai dake arewa masu yammacin kasar.
Maduro, ya kara da cewa an kama dan leken asirin dan kasar Amurka ne a yayinda yake leken asiri a kan matatun man Amuay da Cardon dake jihar Falcon a kasar.
Maduro, wanda bai bayyana sunan wanda ake magana a kansa ba, ya bayyana cewa mutumin da suka kama ma'aikakacin wani jirgin ruwa ne da ke aiki a sansanin CIA a Iraki kuma an kama shi da wasu makamai na zamani da kudi.
Shugaba Maduro ya tabbatar da cewa za'a gudanar da kwararan bincike akan mutumin.
A Venezuela, wani rikici ya barke tsakanin jami’an tsaro da wata kungiya a kan jirgin ruwa a wani gari da ke gabar teku mai nisan mintuna 45 daga Caracas babban birnin kasar a watan Mayu, mutane 8 sun mutu kuma an tsare Amurkawa biyu.
Maduru ya zargi Amurka da Colombiya da lafin shirya rikicin lamarin da kasashen biyu suka musuinta.