Shugaban Kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, za su iya bayar da man fetur a matsayin kudin allurar riga-kafin Corona da su ke yaki da ita.
Maduro ya yi jawabi a tashar talabijin ta kasa inda ya bayar da shawarar su bayar da man fetur su karbi riga-kafin Covid-19.
Maduro ya ce,
"Venezuela na da rijiyoyin man fetur. Muna da masu sayen man fetur. A shirye muke mu karbi riga-kafin Corona mu bayar da man fetur."
Shugaban na Venezeula ya ci gaba da cewa "Mun aika da wasiku ta hanyoyin diplomasiyya. Su ba mu riga-kafin da mu ke bukata, mu kuma mu ba su danyen mai a madadin kudi."
Maduro ya kara da cewa, idan aka amince da wannan shawara tasu, to a shirye su ke da su karbi kaso 20 na alluran da suke bulata waso kwaya miliyan 2,4.
Venezuela ta sayi riga-kafin Corona dubu 100 daga kamfanin Sinopham na China da kuma dubu 100 daga kamfanin Sputnik-V na Rasha.