Hukumomin zabe a kasar sun ayyana shugaban ne a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 28 ga watan Yuli duk da cewa ba a fitar da cikakken sakamakon zaben ba.
Hukumomin zaben dai sun ayyana Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 28 ga watan Yuli, sai dai har ya zuwa yanzu ba su fitar da cikakken sakamako ba, lamarin da ya sa kawayen kasar masu sassaucin ra’ayi wato Colombia da Mexico a ranar Alhamis suka sake nanata kira ga hukumar zabe ta kasar CNE da ta bayyana alkaluman zaben.
'Yan adawar Venezuelan da ke ikirarin cewa sun yi nasara a zaben da aka yi a kasar, sun koka da rashin nasarar, Sakamakon ayyana Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben wanda ya haifar da zanga-zanga a makon da ya gabata da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 24 a cewar kungiyoyin kare hakkin bil adama.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, sama da 'yan kasar Venezuela miliyan bakwai ne suka tsere daga kasar mai mutane miliyan 30 tun bayan da Maduro ya hau karagar mulki a shekarar 2013, akasarinsu zuwa wasu kasashen Latin Amurka da Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI