Uzbekistan ta sanar da cewa sojojinta sun harbo jirgin saman Afghanistan din da ya keta iyakan kasarta.
A cikin sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta fitar, an bayyana cewa rundunonin tsaron na sama sun hana jirgin sojan na sojojin Afghanistan ya keta sararin samaniyar kasar a daren jiya.
A cikin sanarwar an bayyana cewa an fara bincike game da lamarin, kawo yanzu an ba da rahoton cewa ba'a samu hasarar rayuka ba.
Manema labarai sun sanar da cewa jirgin mallakar sojojin Afghanistan ya yi hatsari a yankin Surhanderya na Uzbekistan a kan iyaka da Afghanistan a daren jiya, kuma sojojin Afghanistan biyu da ke cikin jirgin sun ji rauni.