USAID ce ke ɗaukar nauyin mayaƙan Boko Haram - Ɗan majalisar Amurka

USAID ce ke ɗaukar nauyin mayaƙan Boko Haram - Ɗan majalisar Amurka

Perry wanda ɗan jam'iyyar Republican ne mai wakiltar jihar Pennsylvania ya bayyana haka ne a yayin zaman ƙaddamar da Ƙaramin Ƙwamitin Majalisar mai sanya ido kan nagartar Gwamnatin Amurka.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Mista Perry ya ce, ana aika wa ƙungiyoyi irinsu ISIS da Al-Qaeda da Boko Haram kuɗin da ya kai kimanin dala miliyan 697 a kowacce shekara, lamarin da ya bayyana a matsayin ɓarnatar da kuɗaɗen masu baɗa haraji a Amurka.

Kazalika ɗan majalisar ya bayyana shakkunsa kan ingancin rahoton USAID da ke cewa, hukumar ta kashe dala miliyan 136 wajen gina makarantu 120 a Pakistan, yana mai cewa, babu wata hujja da ke tabbatar da wannan iƙirarin nata.

A maimakon haka, ɗan majalisar ya nuna wa USAID yatsa, yana mai cewa, ita ce take ɗaukar nauyin ta'addanci.

Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump ya bada umarnin rufe Hukumar ta USAID bayan ya zarge ta da cin hanci da rashawa. 

Ƙungiyar Boko Haram na ƙaddamar da hare-haren ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma wani ɓangare na ƙasashen Chadi da Nijar da Kamaru da Mali

Wannan ƙungiyar ta ƴan ta'adda ta janyo koma-baya sosai a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin shekaru 15 da ta kwashe tana kai farmaki tare da kashe dubun-dubatan jama'a da suka haɗa da jami'an ƴansanda da sojoji da fararen hula.

Wasu alkalumma sun nuna cewa, sama da ƙananan yara dubu 300 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar hare-haren Boko Haram, sannan kimanin miliyan 2 da dubu 300 sun rasa muhallansu tare da faɗawa cikin ɗimbin matsalolin rayuwa kamar yunwa ko ƙarancin abinci. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)