UNICEF ta yi tanadin sirinjin allurar riga-kafin Corona

Cibiyar Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta bayyana cewar za ta tanadi sirinji guda miliyan 520 don allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19).

Sanarwar da aka fitar daga Asusun  ta bayyana cewar, tuni aka fara shirye-shiryen ganin an raba riga-kafin cutar Corona ba tare da samun matsala a kasashen duniya ba.

Sanarwar ta ce, bayan an kammala aiyukan samar da allurar riga-kafin cutar Corona za nemi bukatar miliyoyin sirinji, a saboda haka Hukumar UNICEF za ta tanadi sirinji kwaya miliyan 520 ashekarar 2021 domin amfani da su a kasashen duniya.


News Source:   ()