UNICEF ta yi kira da a gujewa amfani da kakanan yara a matsayan mayaka a Sudun ta Kudu

UNICEF ta yi kira da a gujewa amfani da kakanan yara a matsayan mayaka a Sudun ta Kudu

Hukumar Asusun Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta nanata kiran da take yi na a gujewa amfani da yara matsayan mayaka a Sudan ta Kudu.

UNICEF a Sudan da Kudu ta bayyana cewa amfani da kakanan yara a matsayan mayaka abin ki ne da kyama kuma lamari ne da ya sabawa dokar kare kananan yara.

A taron da ta gudanar ta yi jan hankali yadda za a kare rayuwar kananan yara daga shiga dukkanin lamurran fitinu a Sudan ta Kudu.

Hukumar ta kara da cewa ya zama wajibi a dakatar da dukkanin miyagun matakan da ke jefa yara cikin hadura iri daban-daban.

Andrea Suley, wakilin UNICEF a Sudan ta Kudu ya yi kira da a dauki matakan kaddamar da shirin da aka kaddamar na kare lafiyar kananan yara a kasar. Tare da kuma kira ga dukkanin kungiyoyi da su gujewa amfani da kananan yara a matsayan mayaka.


News Source:   ()