UNICEF ta yi gargadin karancin ruwan sha a Labanan

UNICEF ta yi gargadin karancin ruwan sha a Labanan

Mutane miliyan 4 a Labanan na iya fuskantar manyan matsaloli wajen samun ruwan sha.

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin tsananin karancin ruwan sha a Labanan.

Dangane da bayanin da Daraktar UNICEF na Labanan Henrietta Fore ta yi ga Kamfanin Dillancin Labarai na Labanan (NNA), akwai yiyuwa mutane miliyan 4 a cikin kasar, galibi yara, za su fuskanci manyan matsaloli wajen samun ruwan sha a cikin kwanaki masu zuwa.

Fore ta jaddada cewa bangarorin ruwa, makamashi da kiwon lafiya suna cikin matsanancin matsin lamba a Labanan, kuma wannan yanayin yana jefa rayuwar ɗan adam cikin haɗari.

Ta ce "Labanan na iya ganin karuwar cututtukan da ake samu daga ruwa." Fore ta ce, tana kira da a samar da makamashi cikin gaggawa a kasar don maido da aiyukan ruwa.

A Labanan, wanda ke fama da rikicin siyasa da na tattalin arziki, ana samun ƙatsewar wutar lantarki na sama da awanni 22 a rana saboda ƙarancin makamashin da ke gudana na tsawon sama da watanni biyu. Katsewar wutar lantarki na ci gaba da yin illa ga duk bangarorin rayuwa.


News Source:   ()