A cikin wannan wasiƙa, ƙungiyoyin sun ce ta hanyar dakatar da wannan yarjejeniya, Tarayyar Turai za ta iya ɗaukar matakan sanya takunkumai a kan manyan jami’an gwamnatin Isra’ila da aka tabbatar da cewa suna da hannu wajen tauye hakki da kuma kisan ma’aikatan yaɗa labarai musamman a yakin Gaza da kuma Gabar Yammacin Kogin Jordan.
An tura wannan wasikar ce zuwa ga shugaban ofishin kare manufofin ƙetare na ƙungiyar EU Joseph Borrell da kuma mataimakinsa Caldis Dombrovskis, tare da jaddada fatan ganin cewa ƙungiyar ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen kisan da ake yi wa ƴan jarida a yankin Falasdinu.
Alƙaluma da Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Ƴan jaridu a duniya suka fitar, na nuni da cewa adadin ma’aikatan yaɗa labarai da suka rasa rayukansu daga ranar 7 ga watan oktoba lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da Hamas ya barke, sun kai 130 yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ƙungiyoyin sun gabatar da wannan wasiƙa ce a daidai lokacin da ministocin harkokin waje na Ƙungiyar ta Turai ke shirin gudanar da taro ranar 29 ga wannan wata na agusta a birnin Brussels. Wasu daga cikin ƙungiyoyin da suka rattaba hannu kan wasiƙar har da Reporters Sans Frontiers, FPU da kuma HRW.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI