Ƙungiyar Hezbollah ta fara janye mayaƙanta daga kudancin Lebanon

Ƙungiyar Hezbollah ta fara janye mayaƙanta daga kudancin Lebanon

Fadlallah ya ƙara da cewar dama can ƙungiyar Hezbollah ba ta ta wata takamaiman sansani ko makamai da ta girke a kudancin Lebanon, kasancewar ta matsayin rundunar yaƙin sunƙuru saɓanin zama wani  ɓangare na sojojin ƙasar.

Ɗan Majalisar yayi waɗannan kalaman ne, a daidai lokacin da rundunar sojin Lebanon ta sanar da fara ƙara yawan dakarunta a kudancin ƙasar, a yayin da dubun dubatar mutanen da suka tsere ke komawa gidajensu bayan da aka ƙulla yarjejeniya tsagaita wuta tsakanin Hezbollah da Isra’ila, watanni biyu bayan ɓarkewar yaƙin tsakanin ɓangarorin biyu.

Rundunar sojin Lebanon ta ce tana aikin tabbatar da tsaro a yankin kudanciin ƙasar ne tare da haɗin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke girke a ƙasar.

Zuwa jiya Laraba, mutane dubu 3 da 823 gwamnatin Lebanon ta ce an kashe, bayan hare-haren da aka riƙa kaiwa tsakanin Hezbollah da Isra’ila daga watan Oktoban shekarar bara, sai dai akasarin mutanen sun rasa rayukansu ne, a ƴan makwannin da suka gabata, bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)