Tarayyar Malaman Islama ta kasa da kasa watau Ulama'u ta yi tir da Allah wadai da tone da kuma lalata kabarin Omar bin Abdulaziz jika ga Khalifa na biyu watau Sayyid na Omar a Idlib din kasar Siriya.
Babban sakataren tarayyar Ali Muhyiddin el-Karadaği ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa,
"Wannan laifi shaida ce dake nuna girman kiyayya ga khalifa Umar bin Abdulaziz, duk da shekaru 1300 bayan rasuwarsa"
Karadağı ya bayyana cewa wadanda suka aikata wannan aika-aikan basu kanance masu cin mutuncin Omer bin Abdulaziz kawai ba, sun kuma kasance suna cin mutunci da zagin akidar Ahl al-Sunnah dama musulmai baki daya.
Ya kuma kara da cewa wannan cin zarafin mataccen bai kasance ba face hari akan Musulmi da kuma niyyar tada zaune tsaye da haifar da fitunu a cikin al'umman Musulmi.
Kafafen sadar da zamunta dake da alaka da gwamnatin Asad a Siriya sun dinga yada bidiyo da hotunan kabarin jikan Halifa na biyu watau Omar bin Abdullaziz fayau. Kabarin da aka tonen kimanin kwanaki goma da suka gabata ba'a san inda aka nufa da gangar jikin Omar bin Abdulaziz ba.