Ulama'u sun yi maraba da sake mayar da Hagia Sophia Masallaci

Ulama'u sun yi maraba da sake mayar da Hagia Sophia Masallaci

Babban sakataren Tarayyar Ulama'u ta kasa da da kasa Ali Muhyiddin el-Karadaği ya bayyana cewar mayar da Hagia Sophia Masallaci na nufin "mayar da gurin ibadan a yanayinsa na ainihi"

Karadaği ya yada a shafinsa na sadar da zumunta inda ya yi sharhi akan Hagia Sophia wanda majalisar ministoci ta mayar gurin ajiye kayan gargajiya a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 1934, matakin da majalisar zartarwa ta soke da kuma sanya hannun shugaban kasa Erdogan aka sake mayar da gurin masallaci a shekaran jiya.

Karadaği, ya bayyana cewa: 

"Masallatan Andalusia an mayar da su cocuna, gurin shan giya da guraren shakatawa da dare, Masallacin Babri dake Indiya an mayar dashi haikali kuma ana yunkurin mayar da Kudus guraren ibadun Yahudawa. Bamu ji suka da kakkausar murya daga yammaci har daga gabashi ba. Amma sai gashi mayar da Hagia Sophia masallaci ya samu suka da nuna kyama da kiyayya daga makiya daga gabashi har ma daga yammaci"

Karadaği a yayin da yake tunatarwa da cewa Hagia Sophia da man Masallaci ne ya kara da cewa, 

"Sarki Fatih Sultan Mehmet da kudinsa ya sayi Hagia Sophia ya kuma sadaukar dashi. Sabili da haka mayar da Hagia Sophia masallaci da kuma bude shi domin fara ibada tamkar mayar dashi a matsayinsa ne na asali"

 


News Source:   www.trt.net.tr