Tarayyar Malaman Adinin Islama ta kasa da kasa ta kalubalanci harin da aka kai filin tashi da saukar jiragen saman Aden dake kasar Yaman abin ta ta bayyana a matsayin "wani mummunan laifi."
Kamar yadda babban sakataren tarayyar Ali Muhyiddin Al Karadagi ya sanar a rubuce 'wannna mumunnan aikin ko ma wane ya aikata shi laifi ne mai girman gake' lafi ne da ya kamata a hukunta wadanda suka aikata shi ba tare da sassauci ba.
Da yake kira da a dauki maytakan kawo karshen rikicin kasar Yaman ya kara da cewa domin kubutar da Yaman daga halin da take ciki ya zama wajibi ga dukkanin al'umma, yan siyasa su bi hanyoyin kyawawa domin kawo karshen matsalar da kasar ke fuskanta.
An dai kai wasu hare-hare inda wasu ababen fashewa uku suka tashi a filin tashi da saukar jiragen saman Aden dake kasar Yaman a shekaran jiya.