Ukraine ta yi wa Moscow mummunan luguden wuta

Ukraine ta yi wa Moscow mummunan luguden wuta

Kazalika wannan harin na Ukraine ya tilasta wa hukumomi sauya aƙalar jiragen sama kimanin 50 a wasu filayen jiragen sama da ke birnin Moscow.

Uku daga cikin filayen jiragen sama huɗu da ke Moscow sun kasance a rufe na tsawon sa’o’i 6 sakamakon luguden da Ukraine ta yi.

Rasha wadda ke kan gaba wajen mallakar makamin nukilya a duniya ta ce, ta yi nasarar lalata akalla hare-haren jirage mara matuka na Ukraine har guda 20 a lokacin da suke gilmawa ta sararin samaniyar Moscow, birnin da ke da yawan al’umma sama da miliyan 21.

Sai dai duk da haka, harin ya yi sanadiyar mutuwar wata mace guda mai shekaru 47, kamar yadda maahukuntan na Rasha suka tabbatar.

Ukraine dai ta yi ruwan hare-haren ne da jirage mara matuka guda 46 a cikin daren da ya gabata, yayin da Rasha ta lalata 38 daga cikinsu.

Wasu mazauna birnin sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, harin ya lalata dogayen bene tare da haddasa gobara a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)