Ukraine ta yi amfani da makaman da Amurka ta bata wajen kai hari cikin Rasha

Ukraine ta yi amfani da makaman da Amurka ta bata wajen kai hari cikin Rasha

Ukraine ta ce ta kai harin ne kan wani rumbun ajiye makaman Rasha mai nisan kilomita 110 zuwa cikin ƙasar, amma bata bayyana samfurin  makaman da ta yi amfani da su wajen kai harin irinsa na farko ba, sai dai wasu ƙwararan majiyoyi sun ce makaman masu linazami ƙirar ATACMS ne da Amurka ta bai wa ƙasar ta Ukraine.

A nata ɓangaren, Rasha ta ce dakarunta sun yi nasarar kakkaɓo biyar daga cikin makaman masu linzami 6 da Ukraine ta harba kan wani sansanin soji da ke yankin Bryansk, yayin da ragowar guda ya afkawa sashin ginin sansanin sojin tare da tayar da gobarar da aka yi gagawar kashewa, ba tare da samun hasarar rai ko rasa dukiya ba.

A farkon makon nan shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya baiwa Ukraine izinin fara amfani da makaman masu linzami masu cin dogon zango na ATACMS da ya tallafa mata dasu, matakin da Rasha ta bayyana a matsayin abinda zai sanya Amurka shiga cikin yaƙin ta Ukraine kai tsaye, lamarin da kuma zai sa ta iya maida mata raddi na matakin soji.

Yaƙin Rasha da Ukraine ya cika kwanaki dubu 1 da ɓarkewa ne a daidai lokacin da kashi 1/5 na faɗin ƙasar ta Ukraine ke hannun Rasha, yayin da kuma a gefe guda, ƙasar  da sauran ƙawayenta suka shiga fargaba kan makomar goyon bayan da Amurka ke bata, da zarar shugaba Donald Trump mai jiran gado ya koma fadar White House.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)