Ukraine ta tsayar da Rasha daga amfani da bututunta wurin aikewa da Gas Turai

Ukraine ta tsayar da Rasha daga amfani da bututunta wurin aikewa da Gas Turai

Ministan makamashi na Ukraine Herman Halushchenko ne ya tabbatar da cewa ƙasar ta dakatar da aikewa da gas ɗin saboda dalilai na tsaro.

Herman a wani saƙonsa ta Telegram ya ce wannan abu ne na tarihi domin Rasha ta rasa kasuwarta, kuma zai kawo mata tazgaro wurin samun kuɗin shiga. Nahiyar Turai ta dakatar da amfani da gas ɗin Rasha kuma wannan ya yi dai dai da matakin da Ukraine ta ɗauka a yau.

A wani taron da aka yi a Brussels a watan da ya gabata shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelenky ya ce Kyiv ba za ta bar Moscow ta ci gaba da samun kuɗi da rayuwar ƴan ƙasar ba, amma ya ce idan har aka riƙe kuɗin gas ɗin har zuwa bayan kammala yaƙin da suke gwabzawa.

Dukda kutsawar da tankokin yaƙin Rasha suka yi zuwa Ukraine gas din Moscow ya ci gaba da bi ta bututun na kyiv ƙarƙashin yarjejeniyar da suka yi ta tsawon shekara 5.

Kafin fara yaƙin, kaso 40 na gas din da Rasha ke sayarwa a nahiyar turai yana bi ta bututun mai guda 4 da suka haɗa da na kogin Baltic da Belarus-Poland da Ukraine da kuma kogin Bahar Aswad.

Bayan fara yaƙin ne Rasha ta tsayar da kusan dukkan gas din da take aikewa ta bututun Baltic da Belarus-Poland.

Katse makamashin na Rasha ya haddasa ƙarancinsa a nahiyar turai. Ƙasashe kamar Jamus sai da suka zuba biliyoyin Yuro domin shigar da gas ta jiragen ruwa, masu amfani da makamashin suka rage saye.

Hakan ya sa ƙasashen Norway da Amurka sun zama manyan masu jigilar makamashin na gas a nahiyar bayan wannan dambarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)