Ukraine ta ce babban makasudin aikin fafutuka da aka kaddamar a watan Agusta kusa da kan iyakarta da Rasha shi ne samar da ajiyar sojojin Rasha domin musanya da fursunonin yaki na Ukraine.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Ukraine ta fitar ta ce "a yayin farmakin, sojojin Ukraine sun kama jami'an Rasha 909.
Ukraine ta kara da cewa "wannan ya sanya aka dawo da daruruwan masu kare Ukraine da aka tsare a gidajen yarin Rasha gida." Kyiv da Moscow har yanzu suna ba da hadin kai kan musayar fursunoni duk da cewa sun shafe kusan shekaru uku suna yaki, kuma Ukraine ta mayar da sojojinta da aka kama a gaba.
A shekarar 2024 dai rundunar sojin Ukraine ta ce dakarunta sun kame sojojin Rasha sama da 700 a wani samame da suka kai a yankin Kursk. Bayan kaddamar da hare-haren ta'addanci,mafi girma da sojojin kasashen waje suka kai a Rasha tun bayan yakin duniya na biyu.
Sojojin Ukraine sun yi asarar yankunan Rasha da suka kwace tun da farko. Kyiv ta ce filin da yake rike da shi a Kursk zai kasance wani muhimmin shirin sasantawa a duk wata tattaunawa ta zaman lafiya da Rasha a nan gaba, wadda dakarunta ke samun ci gaba a fagen daga a gabashin Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI