Ukraine ta sake yin amfani da makami mai linzami na Birtaniya wajen kai hari Rasha

Ukraine ta sake yin amfani da makami mai linzami na Birtaniya wajen kai hari Rasha

Wannan na zuwa ne bayan da Ukraine ɗin da samu damar amfani da nakiyar da ta samu daga ƙasashen yamma wajen hana dakarun Rasha da na Korea ta Arewa yi mata kutse.

Ƴan jarida da dama a ƙasar Rasha sun bada rahoton waɗannan hare-hare a dandalin sada zumunta na Telegram, kuma wani jami’in gwamnatin ƙasar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar laamarin.

Rasha ta ce amfani da makaman yammacin Turai a cikin yankunanta da ke nesa da kan iyaka zai kasance wani mataki na ta’azzara yaƙin, a yayin da ita Ukraine ke cewa tana buƙatar kare kanta ta wajen kai hare-hare sansanonin da Rasha ke amfaani da su wajen karfafa mamayar da ta ke yi mata sama da kwanaki dubu 1 da su ka wuce.

Ƴan jarida Rasha masu ɗaukar rahotanni a kan yaƙin sun wallafa hotunan bidiyo da su ka haɗa da ƙararrakin hare-hare a kan yankin Kursk a dandalin Telegram, inda aka ji fashe-fashe masu ƙarfi aƙalla 14.

Gwamnatin Ukraine ta daɗe tana rokon ƙawayenta na NATO su ba ta damar amfani da makaman da su ka samar mata a kan Rasha, kuma a wannan makon ne shugaba Joe Biden na Amurka ya sahale mata amfani da makaman ATACM, watanni biyu gabanin barin sa karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)