Ukraine ta kama wasu sojojin ƙasar Koriya ta arewa a hannunta

Ukraine ta kama wasu sojojin ƙasar Koriya ta arewa a hannunta

Waɗannan sojoji biyu ne, ko da yake sun sami raunuka, kuma an kawo su Kyiv, Zelensky ya ba da wannan sanarwa ce a shafinsa na sada zumunta da kuma kafofin yaɗa labarun ƙasa.

Pyongyang ta jibge dubban sojojin ta ne domin karfafa sojojin Rasha, ciki har da yankin iyakar Kursk inda Ukraine ta yi kutse a cikin watan Agustan bara.

Ko a watan disambar da ya gabatar Zelensky ya ba da wata sanarwa da ke cewa dakarun ƙasar sa sun samu nasarar kama wasu dakarun Korea ta kudu guda biyu wadda daga bisani suka ce ga garinku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)