Ukraine na ci gaba da zafafa hare-hare a sassan Rasha

Ukraine na ci gaba da zafafa hare-hare a sassan Rasha

Mako guda da ya wuce, dakarun Ukraine sun tsallaka iyakar Rasha, kimanin kilomita 530 daga kudu maso arewacin birnin Moscow, a wani hari mai ban mamaki, wanda shugaba Vladimir Putin ya ce yunƙuri ne na neman matsayi mai ƙwari gabanin tattaunawa, tare da jinkirta kutsawar da dakarun Rashar ke yi.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce na’urorin tsaron sararin samaniyarta sun kakkaɓo tare da lalata jirage marasa matuƙa har guda 12 a yankin Kursk, guda a yankin Belgorod da ƙarin wani a yankin Voronezh.

Jami’an Rasha a yankunan Kursk da Belgorod sun yi kashedi a game da yiwuwar amfani da makamai masu linzami wajen kai hare-hare.

Rasha da Ukraine sun bada  mabanbantan adadi na faɗin ƙasar da suka faɗa ƙarƙashin ikon Ukraine a yanzu, inda a yayin da Ukraine ke iƙirarin ya kai muraba’in kilomita dubu 1, Rasha na cewa bai kai rabin adadin ba.

Har yanzu babu masaniya a game da makomar garin Sudzha, wanda ta nan ne Rasha ta ke tura gas daga Siberia, ta Ukraine, zuwa Slovakia da sauran ƙasashen Tarayyar Turai, amma ya zuwa Litinin, kamfanin Gasprom ya ce yana ci gaba da tura makamashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)