Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayyana cewa Turkiyya zata cigaba da kare muradu da hakkokin Turkawan Meskhetia.
Cavusoglu ya gana da shugaban Tarayyar Meskhetian Turks ta Kasa da Kasa, Ziyatdin Kassanov da wasu manbobin kungiyar.
Kamar yadda minista Cavusoglu ya yada a shafinsa ta Twitter, ya bayyana cewa,
"Zamu ci gaba da kare muradun Turkawan Meskhetian, Wadannan Turkawan 'yan uwanmu ne a duk inda suke sabili da haka zamu ci gaba da basu gudunmowa ta ko wace fanni."