Kasar Turkiyya na ci gaba da taimakon Lebanon bayan munanan fashewar da suka afku a babban birnin kasar Beirut makon jiya.
Da umarnin shugaba Recep Tayip Erdogan za’a bude asibitin da Turkiyya ta gina kimanin shekaru 10 da suka gabata amma ba’a dube ba domin wasu matsaloli.
Shugaba Erdogan ya nada Dkt. Serkan Topaloglu na ma’aikatar lafiya da abincin Turkiyya domin jagoran gudanar da shirye-shiryen bude asibitin da zai fara warkad da marasa lafiya a kasar ta Lebanon.