Turkiyya za ta tanadi allurar rigakafin Korona miliyan 100

Turkiyya za ta tanadi allurar rigakafin Korona miliyan 100

Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dkt. Fahrettin Koca ya bayyana cewa a karshen watan  Mayu Turkiyya za ta shigo da allurar riga-kafin Korona har kwara miliyan 100.

A yayinda Ministan ke jawabi a taron da aka gudanar ta yanar gizo ya bayyana cewa kawo yanzu an shigo da allurar rigakafin Korona na kanfanin Pfizer-BioNTech miliyan 1.4 kuma za’a shigo da miliyan 4.5 a watan Afirilu.

Ya kara da cewa an kuma sarrafa karin allurar rigakafin Pfizer-BioNTech  har kwara miliyan 30 a halin yanzu domin Turkiyya.

Ministan ya bayyana cewa kasar ta fara gwajin wani allurar rigakafin Korona wanda ya kasance daya daga cikin masu inganci a doron kasa.

Ya nanata cewa Turkiyya ta yi kokari wajen samar da allurar rigakafin Korona ta cikin gida wanda jami’ar Erciyes ta sarrafa.


News Source:   ()