Turkiyya za ta gina masallaci a garin Afrin dake Siriya

Turkiyya za ta gina masallaci a garin Afrin dake Siriya

Kungiyar Kare Hakkokin Bil Adama da Bayar da Tallafi ta (IHH) ta kafa tubalin gina Masallaci da zai dauki mutum 500 mai suna Masallacin Afrin Zakirin Ulu a yankin Afrin dake kasar Siriya.

Kamar yadda kungiyar ta sanar mataimakinta Erhan Yemelek ya bayyana cewar an kafa tubalin gina masallacin da aka sa ran za'a kammala a kuma fara ibada a cikinsa cikin shekara guda.

Yemelek wanda ke bayyana cewa akwai karancin Masallatai a yankin garin Afrin ya kara da cewa,

"Musanman a cikin shekaru biyu da suka gabata gwamnatin Turkiyya da kungiyoyi masu zaman kansu sun dauki matakan samar da lumana da inganta lamurkan yankin Afrin akan hakan ne kuma muke kafa tubalin gina masallacin Afrin Zakirin Ulu."

 


News Source:   ()